Nomiis Gee ya halarci wasan motoci wanda Dark Knight Motor Sports suka gudanar a Kano

Photo credit: Dark Knight Motor Sports/Instagram

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Dark Knight Motor Sports sun gudannar da wani babban taro na wasan mota a babban birnin Kano. Wasan wanda za a iya cewa shine na farko a jihar ya samu taron jamma'a daga sassan jihohi da dama. Shirin wasan motocin anyi shi ne cikin tsari duba da cewa an samu daman kare masu kallo daga duk wani abun da zai shafi tsaron rayukan su. 

Hanyoyi Shida Da Zasu Taimaka Ma Wajen Zama Manaja Na Kwarai A Masana'antar Waka

Wasan motocin da aka yi ya nishadantar da masu kallo kwarai da gaske duba da ire-iren samfurin motocin da suka halacci farfajiyan inda aka gudanar da wasan. Abun dai ba a cewa komai saboda direbobin motocin da suka nuna bajintar su a wannan filin, wasun su daga kasashen ketare suka shigo domin ziyartar wasan. 

Banda masu wasan motoci, akwai matukan babura samfurin irin na tsere. Suma sun nuna bajintar su ta wajen yin wasa da baburan su. Matukan baburan ba a bar su a baya ba a inda suka yi shiga mai daukan hankali. 

An samu gayyatar babban mawaki dake zaune a birnin na Kano wato Nomiis Gee wanda da shi aka gudanar da wasan har karshe. Nomiis Gee ya samu daman shiga tseren wasan motar tare da daya daga cikin direbobin masu tukin mai sunan Jay Bash. 

Yanda dakatar da Twitter ya janyo tsaiko ga harkokin mawakan Najeriya da masana'antar

Wasan dai ya kayatar da masu kallo inda a kan ji kururuwar motocin da tafin jamma'a a yayin da masu tukin suka yi wani abun mamaki ko al'ajabi da motocin su. An samu matukan motoci irin su Abdul 44, Nagode daga jihar Kebbi, Argo da dai sauran su. 

Wasan motocin dai an gudanar da shi ne domin nishadantar da al'umma cikin bukukuwan Sallah wanda aka yi. Tabbas jamma'a da dama sun nuna jin dadin su game da shirin kuma suna fatan za a cigaba da gudanar da irin wannan wasan a kai, a kai.

Leave your comment