Illolin Amfani Da Kidan Wasu Mawakan Wajen Rera Wakoki
4 August 2021
By El-Yaqub Isma'il Ibrahim
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Duk wakar da wani mawaki yake so ya rera, tabbas ya kan rera ta ne tare da kida wanda a turance za a iya kiran ta da sunan "instrumental". Instrumental ko a ce salon kida ya kan dauki salo ne daban daban duba da wane irin salon waka shi mawakin yake yi. Ya kan dauki salon rap, hip-hop, R&B, Afro-pop, reggae, jazz, amapiano, salsa da dai sauran su.
Sau dayawa, akwai ire-iren wakokin da suka yi shura sabo da irin salon kidan. Wannan ya kan sa wadu mawaki su yi amfani da kidan wakar wurin dora nasu muryar wanda a kan kira shi da sunan "cover". Yin cover yana da matukar amfani ga wasu mawakan domin ya kan ba da dama duniya su san da irin baiwar da mawakin yake da shi. Sannan kuwa mawakin ya kan yi shura sanadiyar amfani da kidan wakar wanda ya kan sa mawakin ya hadu da mai asalin wakar, ko ya lashe wata gasa ko kyauta, da dai makamancin haka.
Hanyoyi Shida Da Zasu Taimaka Ma Wajen Zama Manaja Na Kwarai A Masana'antar Waka
Amma kuskure na ga mawaki ya yi amfani da kidan wani mawakin ba tare da ya nemi izini ba. Amfani da kidan wani ba tare da izinin sa ba babban laifi ne wanda ya kan janyo a aika mawaki gaban kuliya manta sabo.
Amfani da kidan wani wurin rera waka tamkar satar fasaha ne. Shiyasa manyan mawaka suke yin rajistar wakokin su ga kungiyoyin da zasu kare ayukan su irin su COSON, MCSN, GHAMRO, MCSK, SAMRO, ZAMCOPS da dai sauran su.
Samun shedar hakin mallakin wakoki abu ne mai sauki. Hakin mallaka wanda a turance ake kira da "copyright" wani hanya ne na samun kariya ga duk abun da ya shafi waka face daga lokacin da aka kirkiri wakar har zuwa lokacin da aka fitar da ita a yanayin da za a iya amfani da ita wakar.
A wannan karnin da ake ciki, babban kalubalen da mawaki zai fuskanta idan yayi amfani da kidan wani, sai yazo dora wakar a kan dandalin dora wakoki su ki karbar wakar. Sau da dama su kan dau hukuncin rufe shafin mutum na wani gajeran lokaci ko fiye da hakan. Ga wasu dandalin, sukan bada "copyright strike" a kan shafin mawakin da ya keta dokar da suka tanadar. Amfanin da kidan wani ya kan janyo saiko wurin samun cikkaken mallaki game da asalin wakar ko da kalaman da fikirar rera wakar naka ne.
Hanyoyin Da Mawaki Ya Kamata Ya Bi Domin Bunkasa Sana'ar Sa Guda
Idan har kana so kayi amfani da aikin wani, ya kamata ka nemi izini ga wanda yake da asalin kidan wanda ake kira da sunan "licensing". "Licensing permit" wani sheda ne wanda ke bai wa mawaki dama yayi amfani da wakar da aka yi wa rajista da sharadin za a biya mai asalin wakar wani abu.
Daga karshe, duk wani mawaki mai tasowa ya kamata ya guji yin amfani da kidan wasu mawakan wurin gudanar da ayukan su. Hanya dai mafi sauki shine mawaki ya jajirce wurin samun mai buga kida yayi masa sabon aiki. Moriyar da zai samu nan gaba idan yayi amfani da asalin wakar sa babu iyaka.
Leave your comment