Hanyoyin Da Mawaki Ya Kamata Ya Bi Domin Bunkasa Sana'ar Sa Guda
27 July 2021
Photo Credit: QRY Global Concept
By El-Yaqub Isma'il Ibrahim
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
A yanayin da duniya ke ciki yanzu, mawaka na bukatan abubuwa guda hudu wanda zai karfafa musu gwuiwa a cikin sana’ar su musamman wanda ya shafi nishadi. Sai dai a lokuta da dama, mawaka basu san muhimancin bin wadannan hanyoyi ba wajen neman karin ilimi ba musamman ta bangaren rubuce-rubuce. Zamu duba su dayan bayan daya.
Na daya shine hotuna. Hotuna kan taimaka kwarai da gaske wajen kara kaifin basiran marubuci. Shiyasa tun daga lokacin da ďa ke koyan karatu, hotuna su ne abu na farko da ake amfani da su wajen bunkasa tunanin sa. Hotuna suna da abubuwa da dama dake kunshe a cikin su. Shiyasa akwai karin maganan da ke cewa Hotuna na da dumbun bayanai a ciki wanda a turance a kan ce “Photos speak a thousand words”.
Fitattun record labels 5 dake kasar Najeriya
Na biyu shi ne gogayya wanda a turance ake cewa "experience". Wannan ne ke bambanta babban mawaki daga kanana saboda yawan shekarun da ya dauka a cikin harkar. Gogewa a fannoni daban-daban yana da tasiri a al’amuran shi mawakin.
Na uku shi ne dubiya ko kuwa a ce kallo (a turance wato observation). Abubuwan da ke faruwa kan ba wa mawaki damar juya wannan abun zuwa waka ta hanyar da yake ganin zai iya mika sakon. Wannan kuwa ya danganta da inda abun ya faru, lokacin da abun ke faruwa da kuma hanyar da abun ya faru a idon sa sannan ya kan iya kara nashi abun domin ya inganta labarin ko makamancin haka.
Na hudu shine mawaki ya kamata ya iya ‘kaga ko kuwa in ce iya kwatanta faruwan abu ko bayyana abu a cikin zuciyar sa wanda a turance a kan ce imagination. Wannan tunanin kan zo ko ta fuskar mafarki, ko kwatankwacin haka.
Yanda dakatar da Twitter ya janyo tsaiko ga harkokin mawakan Najeriya da masana'antar
Daga karshe dai, mawaki na bukatar neman karin ilimi a ko yaushe domin ya bunkasa rumbun tunanin sa. Shiyasa a kan ce jahili ba ya zama mawaki. Da fatan mawaka zasu bi wadannan ka'idojin domin bunkasa rumbun tunanin su
Leave your comment