Shahararen Mawaki Sound Sultan Ya Rasu

Photo credit: Sound Sultan/Instagram

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararen mawakin Najeriya  Olarenwaju Fasasi wanda aka fi sannan sa da sunan Sound Sultan ya riga mu gidan gaskiya. Ya rasu ne bayan fama da rashin lafiyar ciwon sankara. Ya rasu ne shekarun sa 44. 

Dan uwan marigayi mawakin, Dakta Kayode Fasasi, ne ya tabbatar da mutuwar Sound Sultan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na yanar gizo ya na mai cewa, a cikin yanayin alhini ne ya ke sanar da mutuwar fitaccen mawakin. Saboda haka ya kamat al'umma su taya su da addu'a sannan su taya su jaje ba tare da tayar da hankalin iyalen nasa da ya bari a baya ba. 

Deezell zai saki sabon fefen mixtape mai taken Vault

Kafin rasuwar sa, ya bar kasar Najeriya zuwa kasar Amurka domin karbar magani watani biyu da suka gabata bayan da gwaji yayi nuni da cewa yana fama da cutar daji na makogwaro a yayin da yaje karbar jinya ta hanyar kemoterapi ko kuwa sankara. 

An haifi Sound Sultan a ranar 27 ga watan Nuwambar shekarar 1977 inda ya mutu sakamakon jinyar cutar dajin makogoro a ranar 11 ga watan Yuli na shekarar 2021 ya na da shekara 44 a duniya. 

Tuni dai mawaka da suka hada da mata da maza suka fara wallafa sakonnin ta’aziyya ga iyalan mamacin a shafukan sada zumunta kamar su Tuwita, Instagram, Facebook da dai suransu. 

Mawaki 442 ya zaki sabuwar waka

Sound Sultan fittacen mawaki ne, mawalafi, makadi, marubuci, jarumi kuma dan kasuwa ne. Ya shigo harkar waka da nishadi a cikin shekarar 1990's a lokacin da yake neman sisi da taro domin biyan kudin aikin situdiyo. A wannan lokacin ne ya saki wakar sa ta farko mai taken Jagbajantis wanda ta zamto bakandamiyar wakar sa a karnin shekara ta 2000.
Daga nan ne  ya samu contragi da Kennis Music a yayin da ya rantama musu hannu. A karkashin su, ya saki kundin fefe guda hudu. Ya yi aiki da Wyclef Jean, 2Face da Faze a inda suka yi aikin wakar Peoud to be African. 

Cikin shekara 2012 Sound Sultan ya zama jakadan wanzar da zaman lafiya karkashin hukumar yankin duniya saboda irin gudumawar da yake bayar wa. Cikin shekar 2015 ya saki wakar Remember bayan ya dau tsawon lokaci bai saki ayuka ba. 

Leave your comment