Namenj zai je kasar Nijar gudanar da wasa.

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa na salon Afro Pop dan garin Ibadan dake yankin yarabawa "Namenj", zai je gudanar da wasa a garin Tahuor da ke kasar Nijar wasa a ranar goma sha bakwai ga watan Uni ta shekara 2021 da mu ke ciki idan Allah ya kaimu.

Sals Fateetee sun yi waka tare da Pheno B dan kasar Nijar

Namenj ya sanar da hakan ne a shafin said na instagram jiya Talata 8 ga watan Uni, inda ya daura hoton wannan taro da za a gudanar a kasar Nijar tare da kira ga masoyan sa da ke kasar Nijar din da su fito kallon sa a cikin wannan wasa da zai gudanar.

Namenj wanda tin bayan da ya saki wakar "Dama" tare da fitaccen mawaki Hamisu Breaker a yan watannin baya ne, Tauraruwar sa ta sake haskakawa fiye da yadda ya ke a baya, kuma mutane da dama su ka fara sanin mawakin.

Fresh Emi ya hadu da mataimakin gwanman Kano

Yanzu haka Namenj na karkashin kwamfanin waka ta Empower da ke karkashin kwanfanin mawaki Mr Eazi. Wanda akwai manyan mawaka irin su Dj Ab da Joeboy a karkashin wannan kwamfanin su ma.

Leave your comment

Top stories

More News