An samu sabon yaron mawaki

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Tinbayan rasuwar fitaccen yaron mawaki dan jahar Kano marigayi "Lil Ameer" an samu tarin yaran mawaka daga jahohi daban daban wadan da su ka fito dan nuna irin ta su basirar, yayin da wa su kuma su ka shigo da salo irin na marifayin, wanda hakan ya sa ba su juma ba aka daina sauraron su saboda su na tuna wa mutane Lil Ameer ne a maimakon su a tuna da su.

Mawakin Hausa Hip Hop Dabo Daprof ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

A baya chan, an yi yaran mawaka irin su Hanny Billy-O, wanda da ne ga shahararren mawakin Hausa Hip Hop kuma jigo a masana'antar Hausa Hip Hop kuma ma'aikaci a radio, wato "Alhaji Bello Ibrahim (Billy-O) ", wanda sun yi zamani tare da marigayi Lol Ameer din. Sai kuma shi "Free Boi Shaba", shima wanda da ne ga fitaccen mawaki kuma ma'akaci a gidan radio da telabijan "Ty Shaban". Sai "Haidar" dan gidan fitaccen mawaki kuma jarumi Adam A. Zango.

Lil Prince ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Sai wa su yaran mawakan su ma irin su "MMT" wanda shima aka fara sa rai da jin sa kwanakin baya, kafin shima aka daina jin shi kuma. Akwai yara irin su "Lil Abdul" dan asalin garin Kaduna. Kuma ko wanne a cikin su ya samu aiki mai inganci daga marikan su daban daban.

Yanzu haka wani sabon yaron mawaki ya fito yanzu daga jahar Niger, mai suna "Afnan", wanda ya saki wakar sa ta farko mai taken "Duniya". Wakar mai dauke da sako akan rayuwa kuma Aminu S. Bono ne ya yi aikin bada umarnin wannan bidiyon, fish ya dauki bidiyon kuma Amart mai kwashewa ya dauki nauyin wannan bidiyon. Tini wakar ta fita kuma har an fara yabon irin basirar yaron mawaki "Afnan".

Leave your comment