Lil Prince ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Photo credit: Feezy's Instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jahar Kaduna, kuma daya daga cikin mawakan dake cikin kunguriyar "Yaron North Side", wato (Y.N.S) Lil Prince ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa a jiya Litinin 24 ga watan Mayu ta shekarar 2021.

Za A Kawo Karshen Gasar Da Rarara Ya Saka

Mawaki Lil Prince ya baiyana hakan ne a shafin sa na instagram, cikin hotunan da ya wallafa, inda ya ke shekada wa masoyan sa cewa yana bikin zagayowar ranar haihuwar sa kuma ya na bukatar su taya shi murna da fatan alheri.

Mawakin wanda yana daga cikin matasan mawaka da ke tashe a jahar Kaduna a halin yanzu, ya fito a cikin wakoki da dama da su ka yi tashe irin su "2019 Cypher", "Da so sa mu ne" da kuma "Ameen". Kuma a cikin wadan nan wakokin ya yi bajinta matuka sosai.

Yk Designer Zai Saki Sabuwar Waka

Mawaki kuma makadi "Feezy" kannin Dj Ab, na daga cikin manya mawakan da su ka daura hoton "Lil Prince" dan Raya shi fatan alheri.

Leave your comment