Mawakin Hausa Hip Hop Dabo Daprof ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop dan jahar Kano, kuma daya daga cikin mawakan dake bada gudunmawa a cikin masana'antar ta Hausa Hip Hop wato "Dabo Daprof", ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa a ranar alhamis 3 ga watan Uni ta shekarar 2021.

An samu sabon yaron mawaki

Mawaki Dabo Daprof ya baiyana hakan ne a shafin sa na instagram, cikin hotunan da ya wallafa, inda ya ke shekada wa masoyan sa cewa yana bikin zagayowar ranar haihuwar sa kuma ya na bukatar su taya shi murna da fatan alheri.

Lil Prince ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Mawakin wanda yana daga cikin manyan mawakan Hausa Hip Hop a wannan zamani, wanda su ke tashe a cikin shekaru goma da su ka wuce kuma har yanzu ake damawa da su. Mawaki Dabo Daprof ya yi wa masoyan sa godiya bisa taya shi murnar karuwa da ya yi na shekaru, sannan ya sheda mu su a cikin kewayen gidajan radio da ya ke cewa zai fara fitar da bidiyo akai akai domin masoyan sa su kara nishadantuwa da shi.

Leave your comment