Deezell mawakin Hausa Hip Hop ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop dan jahar Kano, mazaunin kasar Amurika, kuma daya daga cikin mawakan dake bada gudunmawa a cikin masana'antar ta Hausa Hip Hop wato "Deezell", ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa a ranar Juma'a 4 ga watan Uni ta shekarar 2021.

Mawakin Hausa Hip Hop Dabo Daprof ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Mawaki Deezell ya baiyana hakan ne a shafin sa na instagram, cikin hotunan da ya wallafa, inda ya ke shekada wa masoyan sa cewa yana bikin zagayowar ranar haihuwar sa kuma ya na bukatar su taya shi murna da fatan alheri.

An samu sabon yaron mawaki

Mawakin wanda yana daga cikin manyan mawakan Hausa Hip Hop a wannan zamani, wanda su ke tashe a cikin shekaru biyar da su ka wuce kuma har yanzu ake damawa da su, Deezell ya yi wa masoyan sa godiya bisa taya shi murnar karuwa da ya yi na shekaru, sannan ya sheda mu su kwanan nan zai fara fitar da bidiyon wakar Super Story da ya yi da mawaka ashirin da biyu, cewa zai fara fitar da bidiyo, zai kuma same su ne a shafin sa na YouTube.

Leave your comment