Jaruman Kannywood Sun Yi Taron Shan Ruwa Da Wa'azi.

Picture source:Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

A jiya ne, ranar ashirin ga watan Ramadan, wacce ta yi daidai da biyu ga watan mayu 2021, masana'antar shirye finafinai ta Kannywood ta yi wani gagarimin taro a cikin garin Kano dan yin bude baki tare da wa'azi a kam matsayin fim a addinance da kuma matsayin fim ga tarbiyar al'umma. 

An kaddamar da taron ne a Kannywood TV hall, inda manyan jarumai maza da mata su ka halacci taron dan a gudanar da buda bakin tare da wa'azin da su. Inda su ka gaiyato babban malamin addinin musulinci malam Ibrahim Khalid dan gudanar da wannan lachan.

Tynking Maigashi Ya Saki Sabuwar Waka

Wa su daga cikin sanannun fuskokin da su ka halacci taron sun hadar da
Sani Danja 
Yakubu Muhammad
Ty Shaban
Lawan Ahmad
Lilisko
Da dai sauran su, suma an samu lattar jarumai mata a wajan taron da dama.

Mr Young K Zai Saki Sabon Fefen Bidiyon.

A cikin mawakan da aka yi nishadi da wakokin su, akwai mawakin Hausa Hip Hop Classiq da wakar sa ta "Gargajiya", sai mawakiya "Maryam Fantimoti" a cikin wakar ta mai suna "Ma-aiki".

Leave your comment