Tynking Maigashi Ya Saki Sabuwar Waka

Picture source: Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Daya daga cikin fittattun mawakan Hausa na zamani wanda aka sani da "Tynking Maigashi" ya saki sabuwar waka mai taken "Zanceen Duniya". A cikin wannan makon da mu ka yi bankwana da shi.

Mawakin ya sanar da haka ne a shafin sa na instagram, bayan da ya daura Hoton waka tare da albishir ga masoyan sa kan fitowar wannan sabuwar wakar.

Daso Ta Yi Rabon Kayan Abinci Amadadin Aisha Buhari.

Tynking Maigashi, na daga cikin mawakan da su ke tare da fitaccen mawakin Hausa kuma jarumi Adam A. Zango, kuma ya fito a cikin fefen bidiyon Adam Zango da dama.

Wannan wakar ta Zanceen Duniya, waka ce da ya maida hankali kan rayuwar yau da kullum da kuma dabiyar mutane a zamantakewa. Tini wannan waka ta fita a shafin YouTube na mawaki Tynking Maigashi kuma salon gargajiya aka yi wakar.

Mata Irin Su Mansura Isah Ba Su Da Yawa Yanzu

Leave your comment