Daso Ta Yi Rabon Kayan Abinci Amadadin Aisha Buhari.

Picture source: Daso's Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitacciyar tsohuwar jarumar fim a masana'antar shirya finafinai na Kannywood  Hajiya Saratu Gidado wacce aka fi sani da suna "Daso" ta yi kayan abinci ga malaman addini a jahar Katsina a madadin uwar gidan shugaban kasa Hajiya "Aisha Buhari".

Jaruma Daso ta yi rabon kayan abinci da su ka hadar da kananan buhuhunan Shinkafa, Dawa, Taliya, da sauran su ga mutane kimanin dubu hudu (4,000). Dan tallafa mu su a cikin watan Ramadan.

Jaruma Maryam Ceeter Ta Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwa.

Jarumar ta dauki hotuna daga wajan rabon kayan abincin ga malaman addinin, tare da sheda wa mabiyan ta cewa ta yi rabon ne a madadin gidauniyar matar shugaban kasa mai suna "Future Assured". Wanda ta ke anfani da shi wajan tallafa wa mabukata da kuma ma su karamin karfi.

Daso ta kara banyana cewa ba ita kadai ce ta yi rabon a madadin matar shugaban kasan ba, akwai fitacciyar jaruma Mansura Isah ita ma an bata ta yi rabon ta karkashin kungiyar ta, wanda tini su ka yi wannan rabon a jahohi irin su kanduna da kuma Kano.

Mata irin su Mansura Isah ba su da yawa yanzu. - Mawaki Dabo Daprof

Leave your comment