Mata Irin Su Mansura Isah Ba Su Da Yawa Yanzu

Picture source: Both celebrity's Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop kuma kwararren marubuci daga jahar Kano Dabo Daprof "Mister Ladagoma", ya yi yabo tare da jinjina ga fitacciyar jarumar kannywood Mansura Isah ta shafukan sa na sada zumunta.

Jaruma Maryam Ceeter Ta Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwa.
Mawakin, wanda a halin yanzu ke daga cikin manyan mawakan Hausa Hip Hop da ke jahar Kano kuma mai gabatar da shirye shirye a gidajan radio, ya yi wannan yabon ne sakamakon irin gudunmawar da ya ce jarumar ke baiwa al'umma daga dukuyar da Allah ya ma ta da kuma tallafi da take samu daga daidaikun manyan gidauniya dan ciyarwa tare da koyar da mutane sana'a da kuma aikin hannu, kusanman ga masu bukata ta musanman na nakasa.


Dabo Daprof a cikin kalaman sa ya ce" Hakika Allah ya na zaban wa su daga cikin mutane ya azurta su dan su zamo gata ga wa su mutanan, ni a bincike da nazari na, zan iya cewa Jaruma Mansura Isah na daya daga cikin wadan nan zababbun mutanan. Kuma na fadi haka ne saboda irin rashin gajiyawa da ba ta yi wajan tallafa wa marayu, ma su karamin karamin karfi da kuma nakasassu, kuma babu dare babu rana haka wannan taimakon ke cigaba da gudana duk shekara.

Taaziyar Jaruma Daso Ga Sarkin Kano.

Ina ma a ce a Arewa irin su Mansura Isah su na da yawa sosai, da an samu sauki na matsin rayuwa fiye da yanzu, domin akwai wadan da su ka fi ta samu kuma akwai wadan da su na da dama fiye da ita, sannan Arewa da girma take, shi yasa taimakon yan kalilan daga cikin mutane ba lalle ya yi tasirin da ake bukata ba.

Ina rokon Allah da ya ba ta ladan wannan kokari da ta ke yi da ma ireiren ta, kuma ya sa a yi koyi da wannan kyakkyawar dabiyar ta taimako.

Mansura Isah Ta Koya Wa Nakasassu 50 Aikin Hannu

Leave your comment