Mr Young K Zai Saki Sabon Fefen Bidiyon.

Picture source: Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Daya daga cikin fittattun matasan mawakan Hausa Hip Hop da Afro Pop na zamani, kuma dan jahar Kebbi, wanda aka sani da "Mr Young K" zai saki sabuwar fefen bidiyon wakar sa mai taken "Kece na gani". A cikin wannan makon da mu ka yi bankwana da shi.

Tynking Maigashi Ya Saki Sabuwar Waka

Mawakin ya sanar da haka ne a shafin sa na instagram, bayan da ya daura dan guntun bidiyo daga cikin wakar, tare da albishir ga masoyan sa kan fitowar wannan sabuwar bidiyo.

Mr Young K, na daga cikin mawakan da su ke tare da fitaccen mawakin Hausa na salon Nanaye wato "Ali Jita", a karkashin hadaka da kwanfanin Ali Jita Records da ta Play Bwoy Entertainment, kuma daya daga mawakan da jahar Kebbi ke alfahari da su a halin yanzu.

Mata Irin Su Mansura Isah Ba Su Da Yawa Yanzu

Wannan wakar ta "Kece na gani", waka ce da ke baiyana soyayya da kuma masoya a yayin da aka kamu da so. Tini Young K ya sanar cewa wannan waka za ta fita a shafin YouTube na mawakin nan ba da jumawa ba.

Leave your comment