Genius "Son of Jigawa" Zai Saki Sabuwar Waka.

Picture source:Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Daya daga cikin fittattun matasan mawakan Hausa Hip Hop na zamani, mazaunin jahar Kano kuma dan asalin jahar Jigawa, wanda aka sani da "Genius", wato "Son of Jigawa" kamar yadda ake masa inkiya, zai saki sabuwar waka mai taken "Kati", tare da mawakin gambayar zamani Madox Tbb. 

Mawakin ya sanar da haka ne a shafukan sa na sada zumunci mabanbanta a ranar daya ga watan mayu ta 2021, bayan da ya daura Hoton waka tare da albishir ga masoyan sa kan fitowar wannan sabuwar wakar wacce ya saka ranar sha shida ga wata a matsayin ranar fitowar wannan wakar.

Mr Young K Zai Saki Sabon Fefen Bidiyon.

Genius, na daga cikin mawakan da su ke tare da fitaccen makadin Hausa Hip Hop kuma mawaki "NexceZz BeatZ", kuma ya fito a cikin wakokin mawaka da daba a yan shekarun bayan nan.

Wannan wakar ta "Kati" waka ce da ya maida hankali kan rayuwar yau da kullum da kuma dabiyar mutane a zamantakewa ta bangaran karya, yaudara da fafa wanda matasa maza da mata ke yi. Tini kamar yadda Genius ya sanar, wannan waka zai fita shafin YouTube na mawakin,  da kuma sauran wajajan sauke wakoki.

Tynking Maigashi Ya Saki Sabuwar Waka

Leave your comment