Ricqy Ultra ya saki jerin wakokin dake kunshe cikin aikin Money Over Famous EP

By El-Yaqub I.I

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Ricqy Ultra ya saki jerin wakokin da zai saka cikin gajeren kundi wanda ake kira da EP mai taken Money Over Famous. 

Gajeren kundin mai lakabin M.O.F zai sake shi ne ranar zagayowan haihuwar sa wato 26 ga watan October mai kunshe da wakoki guda biyar. Jerin wakokin da zai saka na kunshe ne da mawaka uku wato Dr Pure, Alobob da Sadiq Astone. 

DJ AB ya saki jerin wakokin da ke cikin sabon kundin aikin Supa EP

Ricqy Ultra yana cin gashin kan sa ne karkashin Qry Musiq wanda shi ne ya dauki nauyin aikin. Simple Touch KefaZz shi ne makadin da ya dauki nauyin sarrafa kida da sauti na wannnan kundin aikin na Money Over Famous. 

Leave your comment