DJ AB ya saki jerin wakokin da ke cikin sabon kundin aikin Supa EP

Photo credit: DJ AB/Instagram 

By El-Yaqub I.I

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

DJ AB na shirin sakin sabon kundin fefen EP mai taken SUPA. Kundin yana kunshe ne da wakoki 8 sannan akwai mawaka biyu wanda ya gayyata a cikin aikin wato MrEazi da Dija. 

Bidiyoyin da aka saka a Arewacin Najeriya cikin Satumba 2021

A cikin jerin wakokin da zai saka, akwai wakar da ta zamo bakandamiya a ciki wato Lukuti. Akwai sabbin wakoki guda bakwai wanda ba a taba jin su ba kunshe a cikin jerin aikin. 

Jerrywine shi ne wanda ya sarrafa sautin aikin baki daya. Zai saki kundin ne ranar 1 ga watan Nuwamba. 

Leave your comment

Top stories