Bidiyoyin da aka saka a Arewacin Najeriya cikin Satumba 2021

By El-Yaqub I.I 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

A cikin watan Satumba mawakan Arewacin Najeriya sun saki wakoki da dama face daga audio zuwa bidiyoyi. Bayan karin ingancin da aka samu wurin sarrafa ire-iren salon wakokin daga makada kwararru, masu bada umarni suma sun nuna bajintar su wurin inganta nasu ayukan. A halin yanzu dai, mawaka sun kara daura dammaran su wajen ganin ayukan su sun fito da inganci saboda masu kallo su nishadantu. Ga dai wakokin da suka yi shura a cikin watan na Satumba. 

9. Rigar So - Lilin Baba

Dab da sakin wannan wakar, ba da jimawa ba yan mata da gayu suka rungumi wannan wakar mai taken Lilin Baba. A halin yanzu dai, Lilin baba ya saka gasa na #rigarso challenge. Ya saki wakar karkashin label din sa mai cin gashin kan sa mai taken NorthEast Records. Ya rera wakar tare da Ummi Rahab sannan Kasheepu shi ne makadin wannan aikin.

 

8. Super story (Episode 5) - Deezell & Numerous artists

Cikin cigaban wakar Superstory wanda Deezell ke jagoranta, ya gayyaci mawaka irin su Cdeeq, Madox, LsVee, Babayanks, Haddy Rappia, Lia, Dabo Daprof,  Bosskid Famous, Khaly Smart, Sarkin Fada, Waekay, Lil Prince, Eimhamy da Big Alhaji. Ovizta shi ne mai shiryawa bayan da Feeiziey shine mai bayar da umarni. 

7. Up 9ja - Bash Neh Pha

Bash Neh 0ha na cigaba da samun daukaka da hazaka lunguna da sakon Arewacin Najeriya. Yana daya daga cikin mawakan da suke sukar gwannati ta cigaba da kula da al'umma ta bangaren tsaro, talauci da dai sauran su. A wannan karon kamun murnar bikin cika shekaru 61 da samun yancin kai da turawan mallaka, Bash Neh Pha ya saki wakar nan mai taken Up 9ja wanda jigon wakar a kan kishin da yake da shi ga kasar sa ta gado (wato Najeriya). Larabeey Films su ne suka ba da umarni wurin aikin.

6. Paracetamol - Larabeey 

Larabeey daya ne daga cikin mawakan da tauraron su na cigaba da haskawa a cikin harkar waka. Mawakin ya fara sakin sabbin ayuka duk cikin mako mai taken Wednesday Freestyle session. A wannan karon, ya saki aikin sa na farko mai taken Paracetamol wanda shi ne ya bada umarni wurin aikin bidiyon. Ku kasance tare da Larabeey duk mako domin Jumma'a da za ta yi kyau, daga Laraba ake gane ta. 

5. Kece Remix - Sojaboy ft IcePrince

Bayan da ya saki asalin wakar shekarar da ta gabata, Sojaboy ya saki wakar Kece Remix a yayin da ya gayyaci mawakin Chocolote City a da wanda ya buda label mai zaman kan sa wato Iceprince Zamani. Jigon wakar a kan soyayya ce. Stanz Media su ne suka bada umarni wurin aikin bidiyon sannan DJ Dammy shi ya sarrafa wakar. 

4. Rukayya - Ali Jita
Ali Jita daya ne daga cikin mawakan da suke cigaba da yin shura a cikin duniyar fagen waka. Ya saki wakar soyayyar nan mai taken Rukayya. Ba abun mamaki b ne ganin yanda mawaka yanzu su kan zabi sunan mace guda sannan su rera waka a kan sunan.  KG Shot It shi ya bada umarni wurin daukar aikin.

3. Excuse Me - Bobby Hai

Karkashi label din sa mai zaman kan sa wato SautiFire, Bobby Hai shahararen mai bada umarni ne a fannin wakoki. Ya saki wakar nan mai taken Excuse me ma'ana, uzuri. Ya shahara wurin yin amfani da raha da barkwanci wajen isar da sakon sa. Shi ne dai ya shirya sannan ya bada umarni wurin aikin bidiyon. 

2. Galadinma - Damzkit ft Iceprince 

Damzkit yana karkashin label na Super Cool Cat wanda Iceprince Zamani yake jagoranta. Damzkit mawaki ne mai tasowa wanda ya saki aikin sa a karo na farko mai taken Galadinma. Jigon wakar a kan soyayya ce sannan Big Shootar shi ya bada umarni.

1. I dey miss you - Skales ft Imanse

Idan baka san cewa Skales dan Arewa ba ne, toh yanzu dai ka san cewa haifaffen jihar Kaduna ne. Mawakin wanda yake karkashin OHK Entertainment ya saki sabon aikin sa mai taken "I dey miss you" wanda a halin yanzu ta ke tashe. Wakar dai ya rera ta ne tare da mawakiya Imanse. 

Leave your comment

Top stories