Zan saki sabon kundin fefe wata mai zuwa, inji Namenj

Photo credit: Namenj/Shazam

By El-Yaqub I.I 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararen mawaki wanda yake karkashin Empawa Namenj ya bayyana a shafin sa na Instagram cewa zai saki sabon kundin aiki wata mai zuwa. 

Namenj wanda ya saki wakoki da dama irin su Fatana, Rai na, Magana, Tare da ke, Watarana, Dama da Ni Dabanne wanda a halin yanzu ta zama daya daga cikin bakandamiyar wakokin sa. 

Bidiyoyin da aka saka a Arewacin Najeriya cikin Satumba 2021

A halin yanzu dai, Namenj yana karkashin Empawa wanda Mr Eazi shi ne madugun kungiyar wanda suke neman mawaka masu fikira domin a tallafa musu. Sun yi aiki da mawaka irin su Joeboy, Killertunes, DJ Neptune, E Kelly da dai sauran su. 

Namenj wanda asalin sunan sa Ali Jubril Namanjo haifaffen babban birnin Ibadan ne wanda ke jihar Oyo. Bayan karasa karatun sa ne ya shiga harkar waka ta hanyar dora murya a kan wakokin wasu wanda ake cewa "cover". Daga nan ne Empawa suka gan kwarewar sa har suka zabe shi a mazaunin wanda zai zama fitilar goshin mawakan Arewacin Najeriya. 

Leave your comment