Ricqy Ultra ya saki sabon aiki mai taken Zuma tare da Lady Hany

Photo Credit: Ricqy Ultra/Instagram 

By El-Yaqub I.I 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Bayan fitowar bakandamiyar wakar su tare da Nomiis Gee mai lakabin Anzo Wurin, Ricqy Ultra ya sake fitowa da wata sabuwar waka mai taken Zuma. 

Ricqy Ultra a wannan karon ya shammaci mabiyan sa domin bai saba yin wakoki tare da mata ba, musammana fannin soyayya. Sai ga shi a wannan karon ya gayyaci matashiyar mawakiya wanda ludayin ta na kan dawo, sannan ita ce ta fito gwana a rukunin hip-hop na mata, Lady Hany cikin wakar nan mai taken Zuma. 

Bidiyoyin da aka saka a Arewacin Najeriya cikin Satumba 2021

Zuma waka ce ta salon hip-hop wanda aka gauraya da salon house music da pop domin a samu abun da zai nishadantar da masu sauraro. Kalamai da jigon wakar duk sun tafi ne a kan soyayya. 

Wakar "Zuma" waka ce wanda Simple Touch KefaZz ya sarrafa aikin sannan Mr Dmej shi ne ya bada umarni wurin aikin bidiyon. 

Leave your comment