Exclusive DJ Mixes and 100% Ad-Free Music!
Yanzu na dawo da karfi na, inji Sojaboy
22 September 2021

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Shahararen mawakin da tauraron sa ke haskawa a halin yanzu Sojaboy ya bayyana wa masoyansa cewa yanzu ya samu sauki sannan ya dawo domin ya kara faranta musu zuciyar su.
Ya bayyana hakan ne a kan shafin sa na Instagram cewa "Yanzu na samu cikaken sauki da kuzari sannan na koma bakin aiki. Ina godiya da addu'ar da kuka yi mun". Ya kammala da cewa "Na koma bakin aiki. Me kuke bukata?"
Fitattun dandalin sada zumunci guda 6 domin tallata hajjar mawaki
A kwanakin baya ne Sojaboy ya dan yi murabus da kan shafukan sada zumunci na dan takaitacen lokaci. Daga nan ne ya rawaito cewa dalilin gujewar sa daga dandalin sada zumunci wanda yayi saboda da rashin lafiyar sa ne. Ya ce "na dan yi fama da rashin lafiya kusan mako biyu sannan an dan samu cece-kuce da kananan maganganu game da rashin lafiya na amma na san cewa yawan ayuka ne da rashin samun hutu shi ne silar. A mazaunin dan Adam wanda ya yarda da ikon Ubangiji, tabbas ya jarabce ni ne da wannan kuma ina masa godiya da hakan. Yanzu dai zan iya cewa Alhamdulillah na warware sannan zan dawo fiye da yanda kuka san ni a da. Godiya nake da addu'ar da kuke yi mun.
A kwanakin baya ne Sojaboy ya saki sabuwar wakar sa wanda yayi gamayya da Iceprince Zamani mai taken Kece Remix.
Weekly Top 10 songs

Tudo Trocado3:17
CHAMPION GAL3:00
ONLY YOU JESUS5:44
Akaana kokukyalo2:21
Joy Is Coming3:08
Nasema3:02
BESTIE2:26
Nigina2:27
Nasema3:02
One time2:32
Top stories
- The Heart of Nachu
10 July
- DC10 INTRO OUT NOW
10 July
- Star nizz
09 July


Leave your comment