M.I Abaga zai saki kundin fefen sa a karkashin Chocolate City

By Khisa CJ

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Bayan da MI Abaga yayi murabus daga kamfanin na Chocolate city a mazaunin mai tafiyar da al'amurorin su (wato C.E.O) a shekarar 2019 bayan da Abuchi Peter ya hau kujerar sa, har yanzu dai yana da yarjejeniya da kamfanin a mazaunin mawakin su. 

Hanyoyi 6 da wakokin ka zasu shahara a dandalin TikTok

A ranar 9 ga watan Satumba,  2021 mashahurin mawaki M.I Abaga ya sanar da cewa ya kammala aikin kundin fefen sa a karo na 11 wanda zai lakana masa da sunan "Project 11". Aikin dai za a sake shi ne bayan da ya saki ayukan Judah EP da The Live Report tare da AQ a shekarun da suka gabata.

Chocolate City sun sanar da cewa M.I Abaga zai saki aikin ne a kan shafin su na sada zumunci bayan da mawakin M.I ya rubuta cewa "Ina ganin na kammala......duk wanda bata yi dadi ba, ku dai yi manaji a hakan....godiya nake da sakkonin da kuka turo. Aikin Project 11 na nan tafe". 

Fitattun Wakokin Arewa Guda 7 Agusta 2021

A halin yanzu dai M.I bai fada menene zai zama sunan aikin ba amma yayi amfani da alamar #undisputed. Bayan da M.I Abaga ya bar kujerar sa a shekarar 2019, ya na karkashin kungiyar a mazaunin mawaki.

Leave your comment