Ricqy Ultra ya samu lambar yabo a Zuru

Photo credit: Ricqy Ultra/Instagram 

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Ricqy Ultra ya samu lambar yabo na musamman a lokacin da ya ziyarci garin Zuru a jihar Kebbi Najeriya. Wannan ya faru ne bayan da matasan garin wanda ake musu kirari da Zuru Classic Ajebutters suka gudanar da taro na musamman domin karrama mutane a fannoni daban-daban. 

Morell ya saki kundin fefen Mansa

Sanannan mawaki Ricqy Ultra wanda ya shahara a bangaren salon Hip-hop ya karbi kyautan na musamman ne duba da irin gudumawar da yake bayarwa a fannin nishadi da karfafa gwuiwar al'umma musamman matasa. 

Ricqy Ultra ya karbi lambar yabon ne kamun nan ya nishadantar da manyan baki da masoyan sa wadanda suka halarci taron.

Scion da Yangaboii ya gayyace BOC, DJ AB, Sojaboy, Blaqshyne da DijayCinch wurin aikin bidiyon sa

An karama mutane da dama a wannan bikin. Kadan daga cikin wadanda aka karrama su ne Sarkin Yarabawan Zuru,  Ibrahim Dan Musa da dai sauran su. Mawakan da suka nishadantar da baki sun kunshi Geleson, Ayasco Gee, KissBee, Sir Billy da dai sauran su. Wannan shine dai karo na farko da aka gudanar da wannan biki na karama jagorai a fannoni daban-daban wanda Zuru Classic Ajeboters karkashin shugan su Khalid Legend suka gudanar. 

Leave your comment

Top stories

More News