Muhimmancin Daukar Bayan Fage A Masana'antar Waka

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Bidiyoyin da ke nuna abubuwan dake gudana a bayan fage wanda aka fi sania turance da “behind the scene” yana da matukar muhimmanci. 

Bayan fage yana kunshe ne da matakan da aka dauka wajen gudannar da aikin bidiyo, yanda aka samu basirar aikin, tsarin da ake bi wurin daukar hoton aikin, na’urorin da aka yi amfani dasu, da dai sauran abubuwa da suka shafi aikin daga farko har zuwa karshe na da matukar tasiri. 

Hanyoyi Shida Da Zasu Taimaka Ma Wajen Zama Manaja Na Kwarai A Masana'antar Waka

Masu bibiya ko kallo sun fi so su gan abubuwan da suka wakana a yayin lokaci da ake gudanar da aikin bidiyon da kuma ganin ingancin aikin a wannan lokacin wanda a nan gaba, ya kan taimaka wajen kara wa aikin martaba da karbuwa ga masu kallo da kuma shi mawakin. 

“Behind the scene” ko kuwa a ce “bayan fage” ba wani sabon abu bane. Yawanci masu kallo kan yi karo da wasu bidiyoyi masu taken “yanda aka yi bidiyon kaza” wanda a turance akan ce “the making”. 

Yanda dakatar da Twitter ya janyo tsaiko ga harkokin mawakan Najeriya da masana'antar

Bayan fage wani abu ne dake kunshe da tsuran hotunan aikin da aka dauka masu motsi wanda ba a tace su ba. Irin wannan bidiyon yana dauke ne da yanda manajojin mawakin ke gudannar da ayukan su, tawagar ma’aikata, al’adar da ake bi wajen aiwatar da aikin, ko kuwa tsarin da ma’aikatan suke bi wajen gudannar da aikin su. 

Tabbas bayan fage na bai wa mawakin wani daman da zai koma yayi nazari a kan ayukan sa musamman wurin gyara kurakuren sa, karin ilimi da kuma hanyar samun kudaden shigowa idan har ya sarrafa aikin hotunan domin ya dora a kan shafin yada hotuna ta yanar gizo da kuma kara tallata kan sa.

Leave your comment