Umar M Shareef zai saki sabon kundin fefen sa

Photo Credit: Umar M Shareef/Instagram 

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Umar M Shareef Shahararen mawakin hausa ne sannan jarumin masana'antar kannywood ne wanda ya shahara a kasar ta Najeriya da sauran kasashen Afirka. 

Umar M Shareef ya bayyana a kafar sada zumunci na Instagram cewa zai saki sabuwar kundin fefe amma yana neman ya ji ra'ayin masoyansa. Ya ce "Ina so in saki sabon album. Ya kuke gani?" 

Yanda dakatar da Twitter ya janyo tsaiko ga harkokin mawakan Najeriya da masana'antar

Sannan a wani sakon da ya kara mannawa ya ce "a cikin sunan maza, wane suna zan wake a sabon album dina". Mutane da dama dai sun zabi sunaye irin su Tukur, Tanko, Faruk,Muhammad, Ahmad, Bilal, Abdul har ma da sunan sa Shareef. 

Daga bisani sai ya tambayi mabiyansa ko wace sunaye a cikin sunayen mata zai wake a cikin sabon album dinsa. Sai mabiyansa suka ambato sunaye irin su Fatima, Aisha, Rukayya, Maryam, Khadijah, Hafsah da Jamila. 

Fitattun record labels 5 dake kasar Najeriya

A halin yanzu dai, bai ambaci menene zai zama sunan kundin fefen aikin ba amma nan ba da jimawa ba, tabbas zai sanar da lokacin da zai saki sabon aikin.

Leave your comment