Lilin Baba zai saki sabin ayuka

Photo credit: Lilin Baba/Instagram 

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Lilin Baba ya tanada wa masoyan sa guzurin wakoki har guda biyu. Ya bayyana hakan ne a shafin sa na Instagram a yayin da ya ce yana shirin sakin wani sabon aiki hade da bidiyo. Ko da dai bai bayyana sunan wakar ko aikin ba amma daga hashtag wanda yayi amfani da shi, akwai mai sunan #DanDamaVideo wanda ke nuni da cewa sunan aikin kenan. 

Fitattun record labels 5 dake kasar Najeriya

Ba a jima da samun sakon ba sai ga shi ya kara bayyana wa masoya cewa akwai wani kunshin aikin da zasu saka banda wanda ya bayyana mai sunan Labarina. 

Ya ruwaito a shafin sa na Instagram da cewa "muna da labarin da zamu gaya muku. Muna muku albishir na wannan aikin mai sunan LABARINA daga @northeastrecords". Ya karasa da sunayen wadanda zasu fito a cikin aikin irin su A Wamba, Aziz, Aliyu, Denzy da Aminu Shadow. 

Yanda dakatar da Twitter ya janyo tsaiko ga harkokin mawakan Najeriya da masana'antar

Lilin Baba ya saki wakoki irin su Ba wata, Taka rawa, Fatima Zarah da Surri. A halin yanzu dai, Lilin Baba yana karkashin label din sa mai sunan NorthEast Records wanda a karkashin sa ne yake sakin ayukan sa.

Leave your comment