Zan saki MANSA ranar 20 ga watan Agusta, inji Morell

PHOTO CREDIT: BBC

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Morell fitaccen mawaki ne wanda ya shahara a bangaren wakoki irin na salon Hip-hop da Afro-pop. Sau dayawa ya bayyana wa masoya cewa zai saki kundin aikin sa amma han bai yiwu ba saboda wasu dalilai. Dan haka ne ya saki wata sabuwar waka hade da bidiyo mai taken MULKI FREESTYLE.

Ina zama dan yin tunani a kan menene so, inji Hamisu Breaker

Morell ya bayyana hakan ne a kan shafin sa na Instagram da cewa "Ganin irin kaunar da kuke nuna mun nace bari na baku tsaraba na musamman domin gazawa na wurin sakin aikin MULKI yau. Na kira abokin aiki na cikin gaggawa domin fito da wannan aikin sai gashi a yau muka dau aikin kuma nan da nan ya tace hoton aikin. Burin mu shine mu fitar da aikin kamun 12 yau kuma mun cimma burin namu." 

Bash Neh Pha da Adam A Zango zasu saki sabon aiki

"Ku kalli bidiyon dai. Zaku lura ina dan cin baki a wasu wuraren saboda ban hadace baitukan wakar ba. Lol! Da fatan zaku nishadantu da wakar. sannan zan saki MULKI ranar 30 ga wata da MANSA ranar 20 ga watan Agusta." 

Sannan ya karashe bayanin sa da cewa "Ina Godiya. Nagooode." 

Morell ya saki fitattun wakoki irin su Aure,  Haba, Kowa, Ba wani Bugatti, Arewa da dai sauran su. 

Leave your comment