Bash Neh Pha da Adam A Zango zasu saki sabon aiki

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Mawakin dake tashe a halin yanzu daga jihar Plateau Bash neh Pha ya hadu da shahararen jarumi kuma mawaki daga masana'antar kannywood Adam A Zango. 

Bash neh Pha ya bayyana hakan ne bayan da ya dora hoto shi da mawakin a kan shafin sa na Instagram. Daga bisani, ya saki gajeren bidiyo wanda ke nunin mawakan biyo suna rera wakar da suka yo aikin ta a cikin studio. 

Ina zama dan yin tunani a kan menene so, inji Hamisu Breaker

Mawakan biyu tare da yan jagoran FKG an nuna su suna ta biye wa wakar da basu riga sun fitar da ita ba a cikin studio. Wakar dai waka ce a kan soyayya duba da yanayin kalaman da aka shimfida a cikin wakar. 

Ya rubuta a shafin sa na Instagram cewa "Ina matukar godiya da gudumawa da kabani. Gaskiya naji dadi sosai. Allah ya saka farin cikin kaman inda ka sani albarkacin annabi Muhammad s.a.w." 

Shahararen Mawaki Sound Sultan Ya Rasu

Bash neh Pha ya saki wakoki irin su Bullet, Mama, yar Alhaji,  Ina so ki sanni, Sai na fada, ku ne mata da dai sauran su. 

Leave your comment