Yakubu Muhammad ya zama jakadar sabuwar gidan kallo a Kano

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawaki, jarumi, mai gaba umarni da kuma shiryawa, "Yakubu Muhammad" ya saka hannu a takarda a matsayin jakadar wata sabuwar gidan kallo na Zamani wato cinema a jahar Kano jiya laraba 10 ga watan Uni ta shekarar 2021.

Fresh Emi ya hadu da mataimakin gwanman Kano

Jarumi Yakubu Muhammad ya sheda wa masoyan sa hakan ne a shafin sa na instagram, bayan wallafa hoton sa da ya yi yana sa hannu a takarda na shedar cewa ya zama cikakken jakadar wannan sabon gidan kallo na zamani da aka bude a Kano, wanda ke kan titin Zaria road, kusa da kantin Jifatu.

Yakubu Muhammad wanda daya ne daga cikin wadan da su ka farfado da harkar gidan kallo na Zamani a Arewa, ta hanyar finafinai da su ke yi da kuma kokarin haska su a cinema, musanman yanda harka fim ta koma yanzu. 

Yk Designer Zai Saki Sabuwar Waka

Ana ganin wannan gidan kallo sun dauki jakadan da ya dace da wannan matsayin, domin Yakubu Muhammad mai mutane ne kuma hakan zai jawo hankalin su izuwa wannan gidan kallon da aka bude sabo.

Leave your comment