DJ AB ya zaki sabuwar waka

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop daga jahar Kaduna, Dj Ab, zai fitar da sabuwar waka mai taken "Lukuti" gobe Juma'a 11 ga watan Uni ta shekarar 2021.

Mawakin ya sheda wa masoyan sa hakan ne ta shafin sa na instagram, ta cikin wani bidiyo mai dauke da mawakin a guri daban daban yana cin abinci a ciki, da ya daura yau da rana, yayin da ya tabbatar da fitowar wannan waka da ya yi karfe sha biyu na rana a manhajojin daban daban na sauke a
Wakoki.

Sals Fateetee sun yi waka tare da Pheno B dan kasar Nijar

Dj Ab wanda ya juma bai saki sabuwar waka ba tasa ta kan sa, kuma haka andan ji ya yi shuru kwana biyu, da alama ya dawo da zafin sa a cikin wannan wakar ta "Lukuti", sunan da wasu ke kiran mawakin yanzu, tin bayan da ya yi kiba kuma su ke ganin sakamakon yawan cin abinci da mawakin ya ke ne ya janyo mai hakan.

Fresh Emi ya hadu da mataimakin gwanman Kano

Dj Ab ya na da mabiya kusan mutun miliyan daya yanzu a shafin instagram, wanda shi ne na biyu a mawakan Hausa Hip Hop da su ka fi kowa yawan mabiya a instagram bayan Deezell wanda shi ne akan gaba har ma da Twitter.

Leave your comment