Dabo Daprof ya yi bikin cika shekara goma sha daya a industry

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawaki marubuci kuma jarumi a masana'antar Hausa Hip Hop da na Kannywood "Dabo Daprof" wanda ake wa lakabi da Mister Ladagoma,  ya yi bikin cika shekara goma sha daya a masana'antar Nishadi da kirkira ta fasaha.

Mutun Dubu Goma Sha Bakwai (17,000) Sun Ga Bidiyon Hamisu Breaker A Ranar Farko.

Anyi wannan biki ne a ranar Asabar biyar ga watan shida shekara ta 2021 a garin Kano, inda mawaka da dama ne su ka halacci wannan gagarimin biki da mawaki Dabo Daprof ya hada. Haka zalika yan jarida da dama ne su ka kalarci bikin kuma an gudanar da abubuwa da dama a wajan wannan taro.

Naziru Sarkin waka ya goyi bayan dakatar da Twitter a Najeriya

Mawaki Dabo Daprof ya kafa tarihi a masana'antar nishadi ta Arewa inda ya zama mutun na farko da ya fara bikin shekarun sa a masana'antar nishadi. Wanda hakan ya burge mutane da dama kuma al'umma da dama su ka baiyana jin dadin su akan wannan abu da Dabo Daprof ya kirkira a Arewa.

Wasu daga cikin manyan mawaka da su ka halarci bikin sun hadar da:
Billy-O
Ty Shaban
Bello Vocal
Nomiss Gee
Ricqy Ultra
Sonikman
Bmeri Aboki
Madox tbb
Son of Jigawa 
DJ Speysh
YK Designer
Jamcy
Queen Zeeshaq
Dan Sa'a
Sulwizzy
Unique Pikin
A-styl dbd
Teddy star boy
M khan
Da dai sauran su

Bmeri Aboki ya kawo ziyarar ba zata ne wajan taron, domin Dabo Daprof bai san zai zo ba,sai Dan Sa'a da ya zo daga Kaduna, haka shima Madox da ya zo daga Zaria.

Akwai gidajan radio da wakilan su da dama su ka zo irin su

Dala FM
Freedom radio
Vision FM
Jalla radio
Sound City
Correct FM
Aminci Radio 
Buk Fm

Da dai sauran su. Anyi taro lafiya kuma mutane da dama sun yaba wa yadda taron ya tsaru.

Leave your comment