Naziru Sarkin waka ya goyi bayan dakatar da Twitter a Najeriya

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin Hausa Nasiru Sarkin Waka ya goyi bayan rufe twitter da aka yi a Najeriya cikin makon nan da mu ke ciki, bayan da kwamfanin Twitter su ka goge wani rubutu da shagaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a shafin sa na Twitter a cikin makon da ya gabata akan ma su tada zaune tsaye na bangarori daban daban a Najeriya.

Lil Prince ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Mawakin ya nuna goyen bayan sa ga hukuncin da gwamnatin najeriya ta yi a shafin sa na instagram, bayan da ya wallafa wani Bidiyo, wanda ke nuna mawakin na rubuta wasika budaddiya ga hukumar lura da gudanar da Twitter da kwamnatin kasa. Tare da jaddada farin cikin sa ga yadda aka dauki mataki akan Twitter bayan da su ka wallafa wani rubutu mai kama da raina kasa.

Ado Gwanja zai saki sabuwar waka da bidiyon ta

Miliyoyin mutane ne ke anfani da shafin Twitter a najeriya, kuma da yawan su sun yi yabo ga wannan hukunci, yayin da wa su ke tunanin hukuncin ya yi tsauri da yawa ace akan mutun daya miliyoyi su shiga matsala. Amma wannan dakatar wa ta yamutsa hazo ba kadan ba, domin shine zancen da ke yawo a ko ina cikin kasar nan da ma wajan ta.

Leave your comment