YK Designer ya fara aikin bidiyon wakar Kina ina

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen matashin mawakin Hausa Hip Hop dan jahar Kano "YK Designer" ya fara aikin bidiyon wakar sa sabuwa mai taken "Kina ina" wacce har yanzu bai sa ranar sakin audio din wakar ba.

An samu sabon yaron mawaki

Mawakin ya fara wannan bidiyon ne a ranar Lahadin da ta gabata 8 ga watan shida ta shekarar 2021. Inda kwararren matashin daracta Umar Oteez ya yi aikin bidiyon. A cikin sanarwar da manajan mawakin Dabo Daprof ya fitar a shafin sa na instagram.

Lil Prince ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

YK Designer wanda ya kasance daya daga cikin mawakan da bidiyon su ya samu karbuwa a cikin shirin Zafafa goma da Nomiss Gee ke gabatarwa a tashar Arewa24. A cikin wakar sa ta "Asa Mana Ganga". Kawo yanzu haka, YK Designer ya na da bidiyo biyar wanda na sa ne na kan sa, wadan da su ka hada da Cover din Gen ta Mayekun, sai wakar Fata na, Asa Mana ganga da Asha rawa sai kuma wannan sabuwar ta Kina ina da za ta fito nan da wani lokacin.

Leave your comment