Mawaki Ahmad Delta zai saki sabuwar waka

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa na salon Nanaye dan jahar Kano, haihuwar jahar Delta, kuma daya daga cikin manyan mawakan Nanaye da ke kan gaba a wajan sakin wakoki ma su tashe "Ahmad Delta" zai saki sabuwar waka tare da fitaccen mawakin Hausa Nura M. Inuwa.

Mawakin Hausa Hip Hop Dabo Daprof ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Wakar mai taken "Gaskiya", shi ne wakar mawaki Ahmad Delta da zai fitar a cikin shekarar nan ta 2021 tare da babban mawaki daga bangaran mawakan Nanaye. ya kuma sanar da hakan ne a shafin sa na instagram, inda ya daura bidiyo yana bin wakar a cikin studio, sannan ya tabbatar wa masoyan sa da cewa wannan wakar zai fito nan ba da jumawa ba.

An samu sabon yaron mawaki

Tin bayan wakar "Kina burgeni", da ta "Kin sace zuciya", da mawaki Ahmad Delta ya saki, tauraron mawakin ya kara haskakawa a cikin masana'antar fim ta Kannywood, Tini masoyan mawaki Ahmad Delta su ka fara banyana ra'ayin su akan wannan sabuwar waka da zai fita, kuma suna ganin ya dace daman ace Ahmad Delta ya fitar da waka tare da wani babban mawakin, domin ya kwana biyu bai saki sabuwar waka ba tare da wani.

Leave your comment