Garzali Miko na neman jarumai da za su fito a sabon fim din shi

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawaki kuma jarumi a masana'antar shirya finafinai ta Kannywood "Garzali Miko" ya yi shelan neman jarumai da ke da ra'ayin shiga sabon shirin fim din sa sabuwa mai taken "Inda rai", wanda za a fara aikin a mako mai zuwa.

Mawakin Hausa Hip Hop Dabo Daprof ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Jarumin ya yi wannan kiran ne a shafin sa na instagram inda ya daura wani bidiyo wanda a ciki yake sanarwa mabiyan sa da duk wani mai ra'ayin ya shiga wannan sabon fim da za su fara dauka wanda labarin sa ya yi daban da sauran labarai da aka saba da su a masana'antar fim ta Kannywood.

Lil Prince ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Garzali Miko wanda a yan kwanakin nan ya dan maida hankali a bangaran wakoki fiye da fim, ya dawo da karfin sa a fanin fim wanda anan jarumin ya fara sanuwa a wajan jama'a. Kuma da alamu jarumin ya shirya gagarumin fim ne wannan karon, domin ganin yadda ya ke neman jarumai da za su fito a cikin wannan sabon fim din. Wanda sai idan an ware makudan kudade a kan fim ne kawai ake gaiyatar jarumai da ke ra'ayin fitowa a cikin fim. Tini masoyan Garzali Miko su ka fara tofa albarkacin bakin su kan wannan fim da jarumin zai fara aikin sa nan da mako mai zuwa.




Leave your comment