Jaruma Hadiza Gabon ta kara shekara daya

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitacciyar jarumar fim a masana'antar shirya finafinai ta Kannywood Hadija Gabon waccen ake wa lakabi da "Yar Maye" ta yi bikin zagayowar ranar haihuwar ta a jiya Talata daya ga watan shida ta shekarar 2021.

Jaruma Hadiza Gabon ta sanar da hakan ne a shafin ta na instagram da Twitter, bayan da ta wallafa wa su hotunan da ta dauka a shagalin bikin zagayowar ranar haihuwar na ta. Inda kuma ta bukaci masoyan ta da su taya ta addua da kuma fatan alheri a shekarun da ta kara.

Mr 442 ya saki sabuwar waka

Hadiza Gabon wacce daya ce daga cikin manyan jaruman Kannywood mata da tauraruwar ta ke haskawa shekara da shekaru yanzu, tin lokacin da ta fito a cikin fim din "Yar Maye", wanda ta taka rawar gani a cikin fim din, har wasu a lokacin su ka dinga fadin cewa daman a gaske Yar Mayen ce.

Mawaki KB Show zai saki fim mai dagon zango

Jaruman Kannywood da mawaka da dama ne su ka taya Hadiza Gabon murnar zagayowar ranar haihuwar ta, tare da ma ta fatan alheri da adduoyi na samun mijin aure na gari domin har yanzu jarunar ba ta yi aure ba tukun. Daga nan muma Mdundo na taya jaruma Hadiza Gabon murnar bikin zagayowar ranar haihuwar ta, tare ma ta fatan alheri.

Leave your comment