Mr 442 ya saki sabuwar waka

Photo credit: Mr 442 Instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen matashin mawaki dan garin Zaria dake jahar Kaduna Mr 442 ya saki sabuwar wakar sa mai taken "Sai Mene" a karshen watan Mayu ta 2021.

Mawakin ya baiyana hakan ne a shafin sa na instagram tare da sanar wa masoyan sa cewa wannan wakar ta "Sai Mene" tiny ya sake ta a shafin sa na YouTube kuma ya na kira da su je su saurari wakar tare yadawa ga sauran mutane.

Har yanzu ba mu hadu da Mr Eazi ba - DJ Ab

Mr 442 wanda a baya bayan nan ne su ka fitar da wakar "Sai Monday" tare da mawaki Madox dan asalin jihar Kano, hakazalika, Mr 442 ya fito a wakar Deezell mai taken "No boyfriend" tare wasu mawakan mutun biyar da Deezell ya saka a cikin wakar.

Larabeey ya saki sabuwar bidiyo

Mr 442 na daga cikin mawakan da ake sauraron su a shafukan sada zumunci da dama a halin yanzu, kuma daga dukkan alamu a shekarar nan ta 2021, mawakin zai ba da mamaki a masana'antar Hausa Hip Hop. Duba da irin wakokin da mawakin ke fitarwa akai akai.

Leave your comment