Har yanzu ba mu hadu da Mr Eazi ba - DJ Ab

Photo credit: DJ Ab Twitter account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin Hausa Hip Hop kuma makadin zamani dan asalin jahar Kaduna Haruna Abdullahi, wanda aka fi sani da "Dj Ab" ya yi yabo ga fitaccen mawakin Afro Pop a Africa dan kasar Najeriya "Mr Eazi", bisa irin gudunmawar da ya ke bashi tin a shekarun baya, duk da kasancewar har yanzu ba su taba haduwa da Mr Eazi din ba ido da ido.

Jarumi Ali Nuhu ya yi murnar zagayowar ranar haihuwar Dan sa

DJ Ab ya sanar da hakan ne yau Talata daya ga watan shida ta shekarar 2021 a shafin sa na Twitter, inda Dj Ab ya shedawa masoyan sa irin gudunnawar da Mr Eazi ya bashi daga sanin sa izuwa yanzu, duk da kuwa a yanar gizogizo kawai su ka hadu da shi, tin bayan lokacin da Dj Ab ya juya wata wakar shi Mr Eazi din mai taken "London Town".

Mawaki Kheengs zai saki sabuwar waka tare da M.I Abaga da Falz

Ya kuma sheda wa mabiyan na sa cewa akwai albishir ta waka da su ka yi tare da shi Mr Eazi din wanda zai fito nan ba da junawa ba, amma kafin nan, zai saki sabuwar waka a cikin wannan watar ta Mayu na 2021. Duk da har yanzu mawaki Dj Ab bai banyana sunan wannan waka ba, amma tini masoyan sai su ka fara tsumayin wannan wakar ta fito.

Muma daga nan Mdundo,  mu na dakon fitowar ta, kuma da zarar ta fito, za mu sada ku da wakar cikin sauki kuma a kyauta ta wannan manhajar ta Mdundo.

Leave your comment