Exclusive DJ Mixes and 100% Ad-Free Music!
Mawaki Kheengs zai saki sabuwar waka tare da M.I Abaga da Falz
1 June 2021

Photo source: Kheengs Facebook page
By Omar Ayuba Isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Shahararren mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jahar Niger da ke zama a garin Abuja "Kheengs" ya sanar da zai saki sabuwar waka mai taken "Who be this guy" tare da manyan mawakan Najeriya biyu mazauna jahar Lagos wato "M.I Abaga" da kuma "Falz".
Ado Gwanja zai saki sabuwar waka da bidiyon ta
Kheengs ya sanar da hakan ne a shafukan sa na sada zumunci a yau Alhamis 31 ga watan Mayu ta 2021, inda ya sanar cewa wannan wakar zai fito a ranar juma'a mai zuwa wanda ya yi daidai da hudu ga sabuwar watan U'nin da za mu shiga ta shekarar 2021. Kuma ya sanar wa masoyan sa da cewa wakar da su ka juma su na tsumayi za ta fito kuma zai sake su a dukkan shafukan sa na zamani.
Lil Prince ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa
Kheengs na daga cikin mawakan Hausa Hip Hop manya da su ka yi waka tare da mawakan kudu manya, banda kheengs, akwai irin su Morell, Classiq, B.O.C, Deezell da Dj Ab, wanda duk sun yi waka da wasu fitattun manyan mawakan kudu irin su M.I Abaga, Phyno, Reminisce, Korede Bello, Dija, Mr Eazi, Magneto, Young Six, Ice Prince, Erma Naira da sauran su. Kuma wannan shi ne ke nuna cigaban da masana'antar Hausa Hip Hop din ke kara samu a shekarun baya bayan nan.
Weekly Top 10 songs

KAPEKE LONDON2:23
BIkola2:58
In My Bed2:50
Buwooma2:44
Ex Nkubilako ft DonMusa2:55
Baddie remix feat Shannnon, aaronix, Tojo3:14
CHAMPION GAL3:00
Paver2:55
Nitampeleka kwa Mama (ft. Xouh)3:44
Joy Is Coming3:08
Top stories
- NEW SONG ALERT
16 May
- Generation
16 May
- Boom Shakatah means
17 May
- Date of birth
15 May


Leave your comment