Larabeey ya saki sabuwar bidiyo

Photo: Deezell Instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen Matashin mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jihar Bauchi Larabeey ya saki sabuwar waka hade da bidiyon ta mai taken "I'm a star" a cikin makon nan da mu ke ciki na watan Mayu ta 2021

Mawaki Hazy D-Star zai saki sabuwar waka

Mawakin ya baiyana hakan ne a shafin sa na instagram tare sauran safukan sa, cewa wannan waka tini ta riga ta fito kuma masoyan sa za su iya zuwa yana gizo su sauke ta tare kallon bidiyon a YouTube, sannan ya bukaci su ma da su bada ta su gudunmawar a wajan yada wa sauran mutane wannan waka ta sa sabuwa.

Matashin mawaki Teddy ya saki waka

Larabeey wanda daya ne daga cikin sanannun mawakan da jahar Bauchi ke ji da su a fannin Hausa Hip Hop ya yi wakoki da dama a baya ciki har da wacce ya yi tare da Classiq mai taken "Antashi", ya kuma fito a cikin wakar hada ka da fitaccen mawaki Deezell ya yi a kwanakin baya. Shima dai Deezell din na daya daga cikin mawakan da su ka nuna ta su gudunmawar tare da goyan baya ga mawaki Larabeey. Ta hanyar daura bidiyon wakar a shafin sa na instagram. Shima Bushkiddo babban mai barkwanci ne a masana'antar nishadi, ya daura wannan bidiyon shima a nashi shafin na instagram.

Leave your comment