Matashin mawaki Teddy ya saki waka

Image source: Teddy's Instagram handle 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Matashin mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jahar Kano da ka fi sani da suna "Teddy" ya saki sabuwar waka tare da bidiyon mai taken "Baby" a cikin makon nan a ranar 27 ga watan Mayu 2021.

Shirin "Izzar So" ta samu yan kallo miliyan daya a kwana goma sha hudu

Matashin ya sanar da hakan ne a shafin sa na instagram bayan da ya wallafa hoton wannan waka da ya saki tare da bidiyon ta, kuma ya ke sanar wa mabiyan sa cewa wannan wakar ya yi ta ne da salo na daban da yadda ya saba waka, kuma ya yi mu su albishir da cewa bidiyon zai kayatar da su idan su ka kalla.

Lil Prince ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

A yan kwanakin baya ne mawakin ya fitar da wani waka mai taken Normalize, wanda Sonikman ya bada umarnin aikin bidiyon, kuma ya bar wa masoyan sa abun fade a cikin bidiyon, domin motar da matashin mawakin ya yi anfani da shi, wato duguwar motar nan mai suna "lemozine", wanda manyan mawaka ne ke sanya irin wanan motar a cikin bidiyon su. Babban mai bada umarni Bello Vocal ne ya ba da umarnin wannan bidiyon.

Leave your comment