Mawaki KB Show zai saki fim mai dagon zango

Photo credit: Kb Show Facebook page 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen matashin mawakin Hausa mai salon wakoki daban daban kuma daya daga cikin mawakan da su ka yi jamiyar kimiya da fasaha ta Wudil da ke jahar Kano, ya sanar da zai saki sabuwar fim mai dogon zango a gobe Alhamis uku ga watan shida ta shekarar 2021 mai taken "Husna yar auta".

Mawakin ya sanar da hakan ne a shafin sa na sada zumunta, inda ya sheda wa masoyan sa cewa gobe da misalin karfe takwas na dare ne wannan fim mai dogon zango zai fito a karo na farko kan tashar YouTube, kuma zai cigaba da zuwa duk sati kamar yadda tsarin fitar da finafinai ma su dogon zango ya ke.

Jarumi Ali Nuhu ya yi murnar zagayowar ranar haihuwar Dan sa

Wannan shine karo na farko da nawaki Kb Show zai fitar da fim kuma nashi na kan shi,  kamar yadda mawakin ya sheda wa wakilin Madubi Naija a zantawar su ta wayar salula a jiya da rana. Kb Show ya tabbatar wa wakilin mu cewa shi ya shirya wannan fim kuma ya dauki nauyin wannan d
Fim, wanda hakan ke nuni da cewa Kb Show na iya zama matashin mawaki na farko da ya fitar da fim na shi na kan shi a masana'antar fim na Kannywood.

Mr 442 ya saki sabuwar waka

Kb Show wanda a kwanakin nan ne ya shirya wani babban wasan sallah a garin sa na asali wato karamar hukumar Danbatta, Inda ya gaiyaci fitattun mawaka irin su Dabo Daprof Mister Ladagoma,  Son of Jigawa, Rio da dai sauran su a bangaran yan Hausa Hip Hop, sai a bangaran mawakan Hausa na salon Nanaye irin su Sayyad Gadan Kaya, malam Ali da dai sauran su.

Wannan fim mai taken "Husna Yar Auta", na dauke da labari mai daukan hankali da kuma fadakarwa tare da nishadantarwa wanda zai ja hankalin mai kallo.

Leave your comment