Ayuba Wezzy da DJ Ab sun saki waka

Photo source: DJ Ab's Instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Matashin mawaki Ayuba Wezzy tare da fitaccen mawakin Hausa Hip Hop Dj Ab sun saki sabuwar waka a cikin makon nan da mu ke bankwana da shi na watan Mayu na shekarar 2021.

Ado Gwanja zai saki sabuwar waka da bidiyon ta

Mawakan biyu sun baiyana hakan ne ta shafukan su na instagram, inda su ke kira ga mabiyan su wajan su nemi wannan sabuwar wakar da tini ta fito a manhajoji daban daban. Wannan shi ne karo na farko da mawakan biyu su ka taba waka tare, kuma duk da karancin mabiyan mawaki Ayuba Wezzy a shafin instagram, amma wannan bai hana su yi waka tare da Dj Ab ba, kuma hakan ya sanya mutane magana akan ko mai ya janyo dalilin da ya sanya su ka yi waka tare. 

Matashin mawaki Teddy ya saki waka

Ana sa ran wannan wakar za su mata bidiyo bayan yan satittuka ma su zuwa, domin bidiyon zai taimaka wajan fito da matashin mawaki Ayuba Wezzy ga masoyan wakokin Hausa Hip Hop. Domin ga mawakin da matashin ne a masana'antar Hausa Hip Hop, bidiyo ne zai iya taimaka ma sa.

Leave your comment