Rikicin Mansura Isah da Sani Danja

Photo Credit Instagram

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitattun jaruman masana'antar shirya finafinai ta Kannywood kuma ma'aurata, wadan da aka fi sani da Sani Danja da matar sa jaruma Mansura Isah sun baiyana ba sa tare a matsayin ma'aurata a halin yanzu.

Matashin mawaki Teddy ya saki waka

Jaruma Mansura ce ta wallafa hakan a shafin ta a na instagram, inda ta shedawa duniya cewa, a halin yanzu babu aren kowa a kan ta, kuma ba sa tare da mijin na ta Sani Danja, wanda daga bisani ta koma ta goge wannan rubutun da ta wallafa tin a baya, sai dai wata majiyar na sheda mana cewa tini jaruma Mansura Isah ta karbi hayan gida inda ta bar gidan Sani Danja kuma tare da yayan su, domin ta tabbata wa duniya cewa ita ba za ta bawa Sani Danja yayan su ba yanzu da su ke kanana.

Shirin "Izzar So" ta samu yan kallo miliyan daya a kwana goma sha hudu

Ma'auratan da su ka yi aure a cikin shekarar 2009, Manyan jarumai ne da ake ganin rabuwar su zai kawo kace nace a masana'antar, duba da irin jumawa da su ka yi tare da kuma yayan da su ka tara su a wannan shekaru 2009 wanda kusan shekara 12 kenan su ka yi a masana'antan.

Muna cigaba da bibiyan wannan al'amari kuma za mu sanar da ku komai gane da gaskiyar wannan Labarin rabuwar wadan nn manyan jaruman.

Leave your comment