DJ Ab na shirin sakin waka

Photo credit: DJ Ab Twitter account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jahar Kaduna Dj Ab da ake wa lakabi da su Babane zai saki sabuwar waka a wata mai kamawa bayan watan Mayun ta shekarar 2021 ta kare.

Ya sheda hakan ne a shafin sa na Twitter, inda ya ce "Sabuwar waka za ta fita nan da wata mai zuwa, kun shiya",tambaya kenan da Dj Ab ya yi wa mabiyan sa, inda tini da dama daga cikin su su ka baiyana jin dadin su ga wannan labarin, kasancewa sun fara korafi cewa gwanin na su Dj Ab ya yi shuru kwana biyu.

Dj Cinch ya samu karramawa

Idan za ku tuna a cikin watanni biyu da su ka wuce, Dj Ab ya saki wani fefen bidiyo da ya yi wakar a salon barkwanci,  wanda abun bai yi wa wasu daga cikin masoyan sa dadi ba. Domin a tinanin su za su ji baituka zafafa irin wacce aka san Dj Ab da ita a baya, sai su ka ga akasin haka.

Lil Prince ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Kuma tin bayan fitowar wannan wakar, Dj Ab bai sake fitar da wani wakan ba izuwa yanzu. Ana ganin shurun irin su Dj Ab a masana'antar Hausa Hip Hop zai iya kawo karyewar gwiwa ga kananan mawaka ma su tasowa wadan da su ke kallon irin Ab a matsayin tsani ko madubin koyi da su.

Leave your comment