Dj Cinch ya samu karramawa

Image source: Dj Cinch Instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen matashin mawakin Hausa na salon Hip Hop mazauni kuma dan asalin jahar Kaduna dake Arewacin Najeriya "Dj Cinch", wanda a cikin makonnin daya ya sanar cewa zai saki sabuwar waka mai taken "Credit alert", ya samu lambar yabo ta karramawa a taron siyasar Kaduna 2021 da aka gudanar ranar lahadi sha uku ga watan Mayu 2021.

AUTA MG BOY Ya Sayi Sabuwar Mota

Mawaki Dj Cinch ya sanar da hakan ne a shafin sa na instagram, a dazu da hantsi a yau Laraba 26 ga watan Mayu na shekarar 2021, inda ya sheda wa masoyan sa da cewa wannan lambar yabo da ya samu babban nasara ce ga wakar da yake yi kuma hakan zai kara daga matsayin sa, musanman idan aka yi la la'akari da daraja da tasiri da wannan taron ke da shi a jahar Kaduna.

Lil Prince ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Tin bayan cin gasar waka da fitaccen makadi Chopsticks da gidan radio ta sound city su ka sa, Dj Cinch ya kara bungasa damar sa wajan fitar da aiyuka daban daban a cikin yan shekarun da mawakin ya samu wannan nasarar.

Leave your comment