Mawakin Ghana Hajji Isquad ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Picture source: Hajji Instagram account 

By Omar Ayuba Isaj

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop dan kasar Ghana, mazaunin birnin Accra, kuma daya daga cikin mawakan dake cikin kungiyar nan na wa da kani ta "I Squad (one blood) wato "Hajji Isquad" ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa a ranar asabar 21 ga watan Mayu ta shekarar 2021.

Lil Prince ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Mawaki Hajji ISquad ya baiyana hakan ne a shafin sa na instagram, cikin hotunan da ya wallafa, inda ya ke shekada wa masoyan sa cewa yana bikin zagayowar ranar haihuwar sa kuma ya na bukatar su taya shi murna da fatan alheri.

Mawakin wanda yana daga cikin manyan mawakan Hausa Hip Hop tare da dan uwan sa Daddy ISquad, wanda su ke tashe a cikin Hausawa da ke kasar Ghana a halin yanzu, ya fito a cikin wakoki da dama da su ka yi tashe tare da dan uwan sa irin su "2
Ramadan", "E be Baba oh" da kuma "Believe".

Mawaki 442 na shirin fitar da sabuwar waka

Mawaki Hajji ISquad ya yi wa masoyan sa godiya bisa taya shi murnar karuwa da ya yi na shekaru.

Leave your comment