Nura M. Inuwa Ya Saki Sabuwar Kundin Wakoki

Photo credit : Nura M. Inuwa instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin Hausa na salon Nanaye a masana'antar shirye finafinai ta Kannywood "Nura M. Inuwa", ya saki sabuwar kundin wakokin da aka juma ana dako mai taken "Ni da ku" 2021 a yau alhamis 17 ga watan Mayu 2021.

Dj Ab Zai Yi Wasan Sallah A Kano

Mawakin ya baiyana hakan ne a shafin sa na instagram bayan da ya daura hoton dake dauke da wakokin da ke cikin kundin, tare da sanarwa mabiyan sa cewa, tini wakar ta fito kuma kai tsaye za su iya zuwa su fara sauke wakokin da nishadantuwa tare da jin sabon salon da mawakin ke dauke da shi a cikin wannan sabon kundin.

Nura M. Inuwa, wanda ya yi wasan sallah da yanmacin yau alhamis a trade fair center dake nan kano ya samu daman fitar da wannan sabon kundin ne bayan bayan da masoyan sa da dama su ka nuna damuwar su bisa junawa da mawakin yayi babu sabuwar waka ko wani aiki sabo.

Kundin Waka - Auta Waziri Ya Fitar Da Sabuwar Kundin Wakokin Sa

Leave your comment