Exclusive DJ Mixes and 100% Ad-Free Music!
Kundin Waka - Auta Waziri Ya Fitar Da Sabuwar Kundin Wakokin Sa
19 May 2021

Photo source : kasheepu instagram account
By Omar Ayuba Isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Fitaccen matashin mawaki kuma dan asalin jahar Kaduna wanda ke wakar Hausa na salon Nanaye, gargajiya da kuma na siyasa, ya sheda wa masoyan sa fitowar sabuwar kundin wakokin sa wacce ya yiwa suna "Wayasan gobe", sanarwar da Auta Waziri ya yi ta shafin sa na instagram, inda ya tabbatar mu su da cewa, zai fitar da sabuwar waka a ranar sallah karama da za a gudanar a watan Mayu ta shekarar 2021
Daga sunan kundin wakokin, ka na iya nazartar cewa wakokin akan rayuwa da soyayya aka yi su, wanda ya hada da bangaran ta na dadi, daci da kuma rabuwa. Sai dai idan mai karatu ya saurari wakokin ne, sai ya tabbatar da ina wakokin su ka dosa.
Dj Ab Zai Yi Wasan Sallah A Kano
Wannan sabuwar kundin ya kunshi wakoki har guda bakwai (7), wadan da su ka hadar da:
1- Tawa
2- Matan Arewa
3- Wayasan Gobe
4- Matan bana ft Ado Gwanja
5- Gaskiyar Zance ft Husaini Danko
6- Ganguna ft Lsvee
7- Zuciya ke kauna
Tini manyan mawaka da kananan su suka daura wannan wakar a shafukan su daban daban dan bada ta su gudunmawar ga mawaki Auta Waziri.
Weekly Top 10 songs

KAPEKE LONDON2:23
BIkola2:58
In My Bed2:50
Buwooma2:44
Ex Nkubilako ft DonMusa2:55
Baddie remix feat Shannnon, aaronix, Tojo3:14
CHAMPION GAL3:00
Paver2:55
Nitampeleka kwa Mama (ft. Xouh)3:44
Joy Is Coming3:08
Top stories
- NEW SONG ALERT
16 May
- Generation
16 May
- Boom Shakatah means
17 May
- Date of birth
15 May


Leave your comment