Mawaki Dabo Daprof ya shammaci mutane a garin Danbatta

Photo source : Instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin Hausa Hip Hop kuma marubuci fitacce Dabo Daprof wanda ake kira Mister Ladagoma, ya shammaci mutane tare da masu shirya wasan sallah, a yayin da ya yi wasan sallah a karamar hukumar Danbatta da ke jahar Kano a ranar daya ga sallah, ranar juma'a 14 ga watan mayu ta 2021.

Tin da farko, masu shirye wasan sallan su ka sanar da zuwan mawakin zai zo garin wasan sallah tare da wasu mawakan a ranar daya ga sallah, sai dai ba su da tabbacin mawakin zai shigo garin wasan sallah, duba da yadda mawakin bai amsa gaiyatar zuwan ba kai tsare ko a shafin sa na instagram bai sanar zai zo ba.

Ali Jita Ya Saki Sabuwar Waka

Amma abun mamakin da ya daure wa masu shirye wasan sallah a garin na danbatta a karkashin jagorancin matashin mawaki KB show, wanda dan asalin garin na danbatta ne, sai ganin Dabo Daprof Kawai aka yi a garin danbatta tare da fitaccen matashin mawaki Genius (Son of Jigawa).

Hakan ya kayatar da masu shirya wasan kuma sun ji dadi matuka, inda aka gudanar da wasan sallan cikin farin ciki da nushuwa ga tarin daruruwan yan kallo.

Deezell Ya Dawo Nigeria Bikin Sallah.

Leave your comment